bbchausa bbchausa

1,473 posts   237,168 followers   55 followings

BBC News Hausa  Shafin BBC Hausa domin sada zumunta da wanzar da muhawara mai amfani. TUNATARWA: Ban da zagi, da batanci da talla a shafin. Mun gode. #bbc #hausa

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya nada tsohuwar Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin daya daga cikin daraktocinsa.

Kamfanin wanda yake da hedkwata a jihar California ta kasar Amurka ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis.

Misis Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko da ta fara zama ministar kudin kasar da kuma ministar harkokin waje a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2006.

Har ila yau ta kara sake zama ministar kudin kasar kuma mai kula da harkokin tattalin arziki a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.

Shugaban kamfanin Omid Kordestani ya ce yana yi wa Misis Okonjo-Iweala da Mista Robert Zoellick, wanda shi ma kamfanin ya dauke shi aiki a matsayin darakta, maraba kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da zababben gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Zababben Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi lokacin da ya karbi shaidar lashe zaben gwamnan jihar a Ekiti ranar Laraba.

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama tare da kishiyar kakarsa Musulma wadda ta haifi mahaifinsa, Sarah Obama a Kenya inda ya je kaddamar da wata cibiyar horaswa ta ‘yar uwarsa Auma Obama a ranar Litinin.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki lokacin da magoya bayansa suka tarbe shi a garin Ilorin na jihar Kwara bayan nasarar da ya samu a kotun koli kwanakin baya.

A ganinku akwai wani abu tsakanin shugaban Faransa da shugabar kasar Croatia?

Mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya na ta yin tsokaci kan ko wanne dalili ne ya sa Shugabar kasar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović ta dinga kasancewa kusa da Shugaban faransa Emmaneul Macron, a yayin wasan karshe na gasar cin kofin duniya, duk kuwa da cewa matar Mista Macron na wajen.

Wasu da dama sun yi ta wallafa hotunan Mista Macron tare da Kolinda Grabar-Kitarović, inda a wurare da dama aka nuna su ko dai suna rungume da juna ko kuma suna sumbatar juna.

Hakan ya sa wasu ma'abota shafukan sada zumunta suka dinga zargin cewa ko dai da wani abu a tsakanin shugabannin biyu ne, yayin da wasu kuma suka dinga jajantawa matar shugaban kasar Faransan.

Shi ma dai mijin shugabar ta Croatia ya halarci wasan. Kawo yanzu babu wani martani daga shugabannin biyu ko kuma gwamnatocinsu.
@parislima ya rubuta cewa: "Emmanuel Macron ya bai wa shugabar kasar Croatia wata dankareriyar sumba yayin da matarsa Brigitte Macron ke ta faman rawa." Shi ma wani mai shafi @nahdhi89 ya rubuta cewa: "Ba zan maki fatan komai ba sai na alkhairi Brigitte Macron." "Ina taya Faransa murnar samun nasara amma gaskiya na ga Brigitte Macron ba ta cikin farin ciki ...@ Ga Emmanuel Macron da shugabar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović," a cewar @SeidGoro.

Wannan sakon na sama kuwa cewa yake: "Me yake faruwa ne da shugaban Faransa da takwararsa ta Croatia? Sai taba juna da sumbatar juna suke yi." A farkon fara wasan dai Shugaba Macron da Shugabar Croatia Kolinda Grabar-Kitarović da na Rasha Vladimir Putin da shugaban hukumar FIFA da Sarkin Qatar na zaune ne daga gaba-gaba, waje na musamman da aka ware musu.
Amma daga bisani sai Sarkin Qatar Tameem bin Hammad Al Thani ya tashi ya nemi matar Mista Macron da ta koma wajensa kusa da mijinta ta zauna, shi kuma ya koma bayansu inda take zaune.

Wasu ma'abota shafukan sada zumuntar dai sun yi ta wadannan kalamai ne suna mai alakanta sabuwar alakar da aka gani tsakanin Mista Macron da shugabar Croatia da yawan shekarun matarsa Brigitte Macron mai shekara 65, shi kuma yana da 45.

Cristiano Ronaldo lokacin gabatar da shi ga magoya bayan kungiyar Juventus a ranar Litinin.

Yadda fada ya barke tsakanin magoya bayan Faransa bayan da ta lashe kofin duniya a kasar Rasha ranar Talata.

Dan wasan Faransa Paul Pogba tare da mahaifiyarsa Yeo lokacin da suke murnar lashe kofin duniya a kasar Rasha ranar Lahadi.

@realalinuhu #russia2018 #worldcup2018 #nigeria #naija
@paulpogba @northern_hibiscuss @opendiariesng @hausaa_fulanii

Faransa ta lashe kofin duniya bayan ta doke Croatia 4-2 #Russia2018 #France #Croatia

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta bayan ya rantsar da Fatuma Ahmed a matsayin mace ta farko kuma Musulmi a mukamin Manjo Janar a rundunar sojin kasar ranar Juma'a.

@realalinuhu #russia2018 #worldcup2018 #nigeria #naija
@realalinuhu @northern_hibiscuss @opendiariesng @hausaa_fulanii

BBC ta gano yadda wasu yan siyasa a jihar Ekiti ke raba kudi ga masu zabe, a jajiberen zaben gwamnan jihar da za a yi ranar Asabar. Mutanen da BBC ta tattauna da su sun ce ana raba musu Naira dubu hudu-hudu. Wasu sun ce APC ta ba su, wasu sun ce PDP ce, wasu sun ce an ba su kudin ne amma aka ce su zabi wanda suke so. Ko kuna ganin sayen mazu zabe ya dace? bbchausa.com #ekitidecides2018 #ekitidecides #ekiti #nigeriapolitics

Most Popular Instagram Hashtags